Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a Bamako babban birnin kasar, dubban mutane sanye da kaya masu dauke da kalolin tutar kasar ne suka taro a wani babban fili, inda suka yi ta rera wakokin kishin kasa da nuna goyon bayansu ga gwamnatin sojojin da ke karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita.
Baya ga Bamako, daya daga cikin manyan biranen Mali da dubban mutanen suka amsa kiran sojojin kasar shi ne Timbuktu da ke arewacin kasar, sai kuma garuruwan Kadiolo da Bougouni da suma ke kudancin kasar.
A makon da ya gabata, shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka cimma matsayar kakaba wa Mali takunkunkumai, tare da rufe iyakokinsu ga kasar, a wani mataki na matsa lamba ga mahukuntan soji na kasar kan su mika mulki ga hannun farar hula, yayin da Amurka da Tarayyar Turai da Faransa kuma suka yi A-wadai da jinkirta zaben sabuwar gwamatin farar hula, tare da nuna cikakken goyon bayansu ga matakin na ECOWAS.
Wannan tsamin dangataka tsakanin sojoji masu mulki a Mali da kuma ECOWAS ta fara ne bayan shawarar da gwamnatin sojin Mali ta gabatar na ci gaba da mulki har na tsawon shekaru biyar kafin gudanar da zabe, yayin da su kuma kasashen duniya suka dage kan sai ta mutunta alkawarin gudanar da zaben a watan Fabrairu da ke tafe.
342/